Matsayin mata a gidajen yarin Pakistan
July 19, 2006Wannan shirin gyara ko ahuwa da shugaba Musharraf ya mika ranar 7 ga wannan wata da muke ciki,bai hada da mata da ake zargi da laifukan kisan kai ko taaddanci ko kuma wasu laifuka da suka shafi kudi ba,kuma dole sai majalisa ta amince kafin ya fara aiki.
Nasir Aslam Zahid,tsohon alkali wanda ya bukaci a soke dokar Hudud a kasar cikin wani rahoton da ya gabatar,ya baiyana cewa,idan ya zuwa ranar 7 ga watan nuwamba majalisar bata amince da wannan doka ba to babu beli ke nan ga masu wadannacan laifuka.
Yanzu haka Zahid wanda ke da wata cibiyar kare hakkokin mata dake babbar gidan fursuna na birnin Karachi,yanyi suka ga wannan umurni da shugaban kasa ya bayar wanda yace ya kamata ya hada da bada belin mata da suka aikata laifin da ya shafi tattalin arziki,hakazalika kungiyoyin kare hakkin bil adama suna ci gaba da kira ayi belin mata da akayiwa fyade kuma aka kama su da laifin aikata zina,karkashin dokokin hudud na kasar ta Pakistan.
A farkon wannan wata ne,shugaba Musharraf ya baiwa majalisar shehunan malaman kasar da suyiwa dokokin gyara,bisa ga dukkan mazhabobi.
Wasu jamian kasar sunce Musharraf ya nuna a niyar gwamnati ce ta soke dokokin gabakidayansu,wanda kuma ya tunzura malaman kasar.
Dokar wadda tsohon shugabvan soji Zia ul Haq ya kafa a 1979,a kokarinsa na kafa shariar musulunci a kasar.
Karkashin dokar dai,mata da akayiwa fyade ana yanke masu hukuncin aiata zina ne,muddin dai baa kama wanda suke zargi yayi masu fyaden ba.
Ayesha Mir wata lauya dake aiki da wata kungiyar kare hakkin mata,tace wannan yunkuri na shugaba Musharraf wani ci gaba ne mai maana ga baiwa mata yancisu,sai dai ta baiyana damuwarta game da sake tsugunad da wadannan mata bayan anyi belinsu ko kuma wane shiri gwamnati take da shi na taimaka masu.
Wani babban batu kuma shine na kudi da zaayi belin matan,wadanda da yawa daga cikinsu ba zasu iya biya ba,saboda haka dole ne su ci gaba da kasancewa cikin kurkuku.