1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsayin Rasha game takunkumi akan Iran

August 13, 2012

Rasha ta soki lamirin Amirka na sanya wa Iran karin takunkuman karya tattalin arziki saboda za su iya yin tasiri kan masana'antunta.

https://p.dw.com/p/15p4c
ARCHIV: Russian President Vladimir Putin (R) meets Iranian President Mahmoud Ahmadinejan for bilateral talks in the UN headquarters in New York, Thursday 15 September 2005. Ahmadinejan and Putin arrived in New York to take part in UN General Assambly. EPA/SERGEI CHIRIKOV +++(c) dpa - Report+++
Hoto: picture-alliance/dpa/dpaweb

Kasar Rasha ta soki matakan da Amirka ta dauka na sanya wa Iran wasu sabbin takunkumai akan bankuna da kanfanonin inshora da kuma sufuri. Fadar mulki ta Moscow da ta ke adawa da matsa wa Iran lamba da ake yi domin ta yi watsi da shirinta na nukiliya, ta danganta yunkuri na Amirka da neman wuce makadi da rawa saboda sun sabawa dokokin kasa da kasa.

Tun da dadewa ne dai Amirka ta katse huldar da Jamhuriyar musulunci ta Iran tare da neman kasashe da ke dasawa da ita sun bi sahunta. Tuni kasashen Japan da koriya ta kudu da Indiya suka rage adadin man da suke saya daga Iran.

Ita dai Rasha ta nunar da cewa matakan baya bayannan da Amirka ta dauka akan Iran suna na iya yin tasiri akan kanfanoninta. Da ma dai Moscow da Washington sun farfado da dangartakarsu ne bayan hawan Barack Obama kan kujerar mulki. Sai dai hulda tsakanin kasashen biyu ya sake tsami sakamakon rarrabuwar kawuna da ake samu tsakaninsu game da rikcin siriya, da kuma zargin Amirka da shisshigi a harkokinta na cikin gida da Rasha ke yi.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Usman Shehu Usman