1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsayin tsarin mulkin Najeriya dangane da barin jam'iyyar siyasa

January 21, 2014

Dokokin Najeriya sun bai wa 'yan majalisun dokoki ko kuma gwamnoni damar ficewa daga jam'iyyun da aka zabesu idan har suna fama da rigingimun cikin gida.

https://p.dw.com/p/1AuLP
Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Hoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Tsarin mulkin Najeriya ya bai wa ko dai 'yan majalisar dokoki ko kuma gwamnoni damar ficewa daga jam'iyyar da aka zabesu a karkashinta, muddin dai jam'iyyar tana fuskantar rigingimu ko kuma ta rushe.

Masana harkokin shari'a sun nunar da cewar inda za a fuskanci matsala shi ne idan jam'iyya na dunkule, babu rarrabuwar kawuna a cikinta.

Domin karin bayani, za ku iya sauraren shirin a kasa.

Mawallafi :  Saleh Umar Saleh

Edita        :  Abdourahamane  Hassane