1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsin rayuwa na kara kamari a kasashen Afirka

Lateefa Mustapha Ja'afar MA
May 17, 2022

Kungiyoyin agaji na duniya, na gargadi kan yiwuwar matsalar yunwar da wahalhalu da ake ciki a yankin kusurwar Afirka ta karu. Farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabi.

https://p.dw.com/p/4BQsH
Symbolbild Afrika Markt Bunt
Hoto: C. de Souza/AFP/Getty Images

A birnin Nairobi fadar gwamnatin Kenya, kananan shaguna na gasa burodin da ake kira da Chapati da al'ummar kasar suka saba yin karin kumallo da shi. Sai dai a yanzu mutane da dama ba sa iya saye sakamakon tsadar da ya yi inda farashin Chapati ya ninka sau biyu abin da ya haifar da tsadar rayuwa. Tsadar hajar dai ba ta rasa nasaba da yadda alkama da naman girki ya yi tashin gwauron zabi a kasuwanni. 

Kasar Kenya dai na shigar da kimanin kaso daya bisa uku na alkama daga kasar Rasha da Ukraine. Sakamakon tashin gwauron zabin da farashin alkamar ya yi a kasuwannin duniya, ya sanya farashin burodi ya karu a babban gidan burodin Nairobi na Kenafric da ke samarwa da manyan kantunan sayar da kayan masarufi burodi. Ba kasar Kenya ce kawai ke fama da tarin matsalolin tsadar rayuwa a yankin na kuryar Afirka da ma kudancin nahiyar ba, har ma da kasashen Zimbabuwe da ke fama da tsadar farashin man fetur da kuma ta shafi rayuwar al'uma.

Sudan Khartum Bäckerei Brot
Hoto: Getty Images/AFP/A. Shazly

Haka ma abin yake a Somaliya, inda shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya,  ya nunar da cewa farashin kayayyaki a gabashin Afirka na hauhawa cikin gaggawa.

A cewar Theresa Anderson, shugabar sashen kula da sauyin yanayi na kungiyar Actionaid da ke yaki da talauci da rashin adalci, kasashen Afirka da dama na bukatar tallafi sakamakon annobar Corona da matsalar sauyin yanayi baya ga bukatar agajin gaggawa sakamakon rikicin siyasa da masassarar tattalin arziki da kuma tashe-tashen hankula.

Shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya, ya nunar da cewa akwai kimanin mutane miliyan shida da ke fama da matsananciyar yunwa a kasar Kenya, daga cikin su akwai kananan yara miliyan daya da dubu 400. Hakan dai na nuni da cewa akwai yiwuwar kasar ta afka cikin gagarumar matsalar karancin abinci in har kungiyoyin bayar da agajin gaggawa ba su samu dauki ba.

Akwai yiwuwar kasashe da dama su afka cikin matsalar yunwa in har ba a dauki maataki ba, kuma kasashen da za su fi fuskantar matsalar, su ne na nahiyar Afirka musamman ma yankin kuryar Afirka. Su ma dai kasashen yankin yammacin Afirka ka iya fuskantar wannan matsala, ta la'akari da yadda suke fama da matsalar hare-haren 'yan ta'adda da ke janyo karuwar 'yan gudun hijira da kuma bukatar kai dauki na gaggawa.