Matuka jiragen Lufthansa za su janye yajin aiki
November 26, 2016Talla
Sabon tayin na Lufhansan na da nufin warware takaddama da matuka jiragen, da ke yajin aiki tun daga ranar Laraba. Yajin aikin na wannan makon wanda ke zama na 14 irinsa kama daga shekara ta 2014, ya gurgunta ayyukan kamfanin da ya soke jirage wajen 2,600, batu da ya shafi pasinjoji sama da dubu 315.
Matuka jiragen na Lufhansa dai a baya, sun yi barazanar fadada yajin aikin nasu fiye da yau7 Asabar, batu daya haifar da damuwa a zukatan masu zuba jari, saboda dumbin asarar da kamfanin zai yi, dama barazanarsa ga tattalin arzikin Jamus da ke zama kasa mafi karfi a nahiyar Turai, a fannin tattali.
A daren jiya Juma'a ce dai, kungiyar matuka jiragen na Lufthansa suka sanar da cewar, ba su da niyyar fadada yajin aikin fiye da yau Asabar.