1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi bikin girmama marigayi Mandela

Ramatu Garba Baba
December 3, 2018

Dubban dubata sun hallaci bikin girmama marigayi Nelson Mandela da ya kafa tarihi bayan da ya jagoranci fafutukar ganin bayan wariyar launin fata a kasar Afirka ta Kudu.

https://p.dw.com/p/39Ilv
Südafrika Johannesburg "Global Citizen Festival Mandela 100"
Hoto: picture-alliance/BELGA/B. Doppagne

Daga cikin shahararrun mawakan zamani da suka hallaci taron, akwai mawakiyar Amirka Beyonce da mijinta Jay Z da kuma kuma mawaka Pharrel Williams da Ed Shareen da sauransu. Mawakan sun kwashi dogon lokaci suna nishadantar da jama'a da suka yi dandazo a wajen bikin da aka tsara a karkashin jagorancin gidauniyar Global Citizen.

Bikin ya zo daidai da cika shekaru dari na haihuwar gwarzon da ya taka muhinmmiyar rawa a kawo sauyi ta hanyar samar da daidaito a tsakanin bakake da fararen fata a kasar. Ana son anfani da tallafin da za a samu daga bikin a ayyuka na yaki da talauci da yunwa da kuma rashin daidaito a tsakanin al'umma. Bikin ya sami halartar manyan 'yan siyasa da shugabanin kasashen Ghana da Ruwanda da Saliyo. Shugaban bankin duniya Jim Kim ya sanar da bayar da tallafin na dala biliyan daya.