1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mawuyacin hali a Aleppo sakamakon gumurzu babu kakkautawa

Mohammad Nasiru AwalAugust 9, 2016

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi game da tabarbarewar rayuwa a birnin Aleppo.

https://p.dw.com/p/1JevZ
Aleppo Syrien Evakuierung humanitäre Hilfe Luftangriff Russland
Hoto: picture-alliance/dpa/A.H.Ubeyd

Jami'an Majalisar Dinkin Duniya sun ce mawuyacin halin da mazauna birnin Aleppo da kewaye na kasar Siriya ke ciki yana kara tabarbarewa, yayin da yawan mutanen da ke tserewa daga yankin ke karuwa. A jawabin da ya yi ga manema labarai a birnin Geneva kakakin ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya Jens Laerke ya ce halin da ake ciki a Aleppo na da wahalar gaske.

"Damuwarmu a yau ta shafi ilahirin birnin Aleppo da kewaye inda muke da mutane kimanin miliyan biyu da ba su da ruwan sha da hasken wutar lantarki. Ana cikin wani yanayin zafin rana mai kuna, saboda cunkoson mutane akwai barazanar barkewar cututtuka."

Jami'in ya yi kira da a tsagaita wuta nan-take don samun sukunin kai kayan taimakon jin kai ga mabukata.