1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mawuyacin hali da Iyaye ke ciki a Chibok

Abdurraheem HassanOctober 15, 2014

Watanni shida bayan sace yara matan sakandare a garin Chibok da ke jihar Borno, 'yan uwa da iyayensu na ci-gaba da juyayi, ba tare da sanin halin da suke ciki ba.

https://p.dw.com/p/1DW6n
Mutter des Chibok-Mädchens
Hoto: DW/Abdul-raheem Hassan

A kwana a tashi a wannan Talatar ce aka cika rabin shekara da Kungiyar Boko Haram ta sace 'yan mata 'yan makaranta sama da 200 a garin Chibok dake cikin jihar Borno a yanki arewa maso gabashin Tarrayar Najeriya.

Iyayen wannan 'yan mata da 'yan kungiyar fafutukar ta Boko Haram ke ci gaba da yin garkuwa da su dai, na cikin mawuyacin hali. Lamarin da ke zama cuta a zukatan iyayen da ma sauran al'umma. Hada da haddasa al'amura marasa dadi ga iyalan daliban da aka sace a makarantar ta Chibok.

Yawaita tunani dai shi ne babbar cutar da ke addabar iyalan, na rashin sanin halin da 'ya'yan nasu ke ciki. Inda hakan ne ke haddasa wasu kamuwa da cuituttuka da ke da nasaba da bugun zuciya ko kuma hawan jini.

A ziyarar da wakilin DW Abdurraheem Hassan ya kai a garin na Chibok inda ya yi hira da wasu iyayen, sun bayyana bakin cikinsu dangane da rashin yaran nasu, tare da kira ga hukumomi da ma 'yan Boko Haram a kan su dube su da idon rahama.