Har yanzu ana cin zarafin jama'a a Burundi
September 18, 2020Talla
Sabon rahoton da kwamitin binciken ya fitar kan Burundi yace fatan da jama'a suka nuna a karshen mulkin shekaru 15 na marigayi tsohon shugaban kasar Pierre Nkurunziza ya gushe yayin da aka cigaba da cin zarafin al'umma tun bayan da shugaba Evariste Ndayishimiye ya hau karagar mulki a watan Juni.
Shugaban kwamitin Doudou Diene yace basu ga wani sauyi ba kawo yanzu.
Burundi ta fada cikin rikici tun shekarar 2015 lokacin da Nkurunziza ya nemi yin tazarce karo na uku ya kuma lashe zaben da 'yan adawa da dama suka kaurace masa.