1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tasirin Covid-19 na haifar da tabin hankali

May 14, 2020

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira ga kasashen duniya da su mayar da hankali sosai wurin tabbatar da lafiyar kwakwalwa a wannan lokaci na coronavirus.

https://p.dw.com/p/3cBw4
Antonio Guterres PK Covid-19
Hoto: webtv.un.org

Antonio Guterres a cikin wani sabon rahoto mai taken ''cutar corona da bukatar samar da lafiyar kwakwalwa'' ya ce a yanzu cutar tana haddasa wa iyalai da al'ummomi matsalar tabin hankali. A cikin wani bidiyo da ya fitar daga birnin New York Sakatare Janar din ya ce: 

''Cutar Covid-19 ba wai lafiyar jama'a ta fili kadai ta ke tabawa ba, ta na kuma kara haifar da damuwa ga kwakwalwa. Bakin cikin mutuwar 'yan uwa da abokai da bacin rai daga rasa ayyukanyi da kebe mutane gami da kulle mutane a cikin doka suna haifar wa jama'a rashin tabbas ga makomarsu a wannan lokaci na coronavirus.''