1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karuwar hukuncin kisa

Zainab Mohammed Abubakar
April 4, 2023

Hukumar kare hakkin bil adama ta MDD ta yi Allah wadaran karuwar hukuncin kisa a Iran, ciki har da wadanda ke da hannu a zanga-zangar kasar.

https://p.dw.com/p/4PgbE
Belgien Protest von Exil-Iranern in Brüssel
Hoto: Johanna Geron/REUTERS

Hukumar ta amince da wani kuduri da ke nuna matukar damuwa kan yadda ake samun karuwar mutanen da ake kashewa ta wannan hanya, ciki har da mutanen da aka yanke wa hukuncin kisa saboda zargin su da hannu a zanga-zangar baya-bayan nan.

Kudirin wanda kazalika ya kara wa'adin mai bada rahoto na musamman na Majalisar Dinkin Duniya kan harkokin kare hakkin bil adama a Iran da tsawon shekara guda, ya samu kuri'un amincewa 23 daga cikin wakilan hukumar 47.

Wasu wakilai 6 sun kaurace wa kada kuri'ar, a yayin da China da Cuba da Pakistan da Vietnam suka kasancve cikin kasashe 8 da suka yi adawa da wannan mataki.

Kudurin ya yi nuni da kakkausar suka daga kasashen duniya kan murkushe masu zanga-zangar da kasar ta Iran ta yi a watan Satumban bara.