Kasashe na fifita kawunansu a yaki da Covid-19
June 27, 2020A wata hira ta musamman da DW Mataimakiyar Shugabar Majalisar Amina Mohammed ta ce coronavirus na bukatar a hada kai don a yake ta bil hakki da gaskiya. Mohammed ta ce sabanin haka akasarin kasashen duniya sun yi kokarin magance matsalar a cikin gida ba tare da kokarin kawo wa gabadaya duniya maslaha ba.
''Corona na wanzuwa a kowane bangare na duniya, kuma kowa na cikin barazanar kamuwa da ita. A saboda haka abu ne da ke bukatar kasashen duniya su hadu don nemawa kai mafita. To amma sai muka gano cewa kowa ya koma gefe guda yana nemawa kansa hanyar da za ta fusshe shi.'' in ji Amina Mohammed.
Amina Mohammed 'yar Najeriya ta yi wannan hira da DW albarkacin cika shekaru 75 da kafa MDD, inda ta ce suna sane da cewa samun kasashe 193 na duniya su yi magana da murya daya, abu ne mai wahala amma suna kokarin shawo kan wadanda ke kokarin kaucewa daga wannan turba don magance corona, cutar duniya.