Fada na kara yin muni a Afghanistan
August 5, 2021Talla
Gwamnatin Afghanistan ce ta gabatar da bukatar yin taron tare da sauran kasashe, Nowai da Estoniya, yanzu haka 'yan Taliban na gwabza kazamin fada tsakaninsu da dakarun gwamnati a manyan garuruwa a ciki har da Heirat da ke kan iyaka da Iran da kuma Kandahar da ke a yankin kudanci. Yakin ya kara yin muni ne bayan da dakarun Amirka da na sauran kasashen duniya suka fara ficewa daga Afghnistan din.