1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dinkin Duniya ta nemi Rasha ta janye daga Ukraine

Suleiman Babayo ZMA
March 2, 2022

Kuri'ar da aka kada a babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci Rasha ta kawo karshen kutsen da ta kaddamar a kan Ukraine.

https://p.dw.com/p/47up5
USA | UN Generalversammlung zum Krieg in der Ukraine
Hoto: Seth Wenig/AP Photo/picture alliance

Babban zauren Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ya kada kuri'a da gagarumin rinjaye na neman Rasha ta janye daga kutsen da ta kaddamar a kan Ukraine, wajen tsaida fada da janye dakaru, matakin da zai mayar da Rasha saniyar ware idan ta yi kunnen kashi na kin mutunta kudirin.

Yayin kada kuri'ar kasashe mambobi 141 daga cikin 193 suka amince da wannan kudiri na Majalisar Dinkin Duniya lokaci zaman babban zaure na ba kasafai ba, da aka yi samakaon amincewa da haka daga Kwamitin Sulhu na Majalisar ta Dinkin Duniya. Lokaci na karshe da aka yi irin wannan taron gaggawa shi ne a shekarar 1982.