MDD ta bukaci binciken harin Idlib a Siriya
October 28, 2016Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya yi kiran gudanar da bincike cikin gaggawa kan harin da aka kai wata makaranta a birnin Idlib na kasar Siriya, harin da asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniyar UNICEF ya ce shi ne irinsa mafi muni da aka kai cikin shekaru shida da aka yi ana yakin. Asusun na UNICEF ya ce yawan wadanda suka rasu a harin ya karu zuwa mutune 28 dwadana suka hada da yara 22 da kuma malamai shida.
A cikin wata sanarwa da ya fitar Ban Ki Moon ya ce harin wanda aka kai yankin da ke karkashin yan tawaye ka iya zama laifin yaki idan aka tabbatar da cewa an aikata shi ne da gangan. Wasu wadanda suka shaidar da lamarin sun ce jiragen yaki sun kai hari musamman a garin Hassa har sau goma. Yan adawa sun dora alhakin harin a kan Rasha da kuma jiragen yaki na gwamnatin siriya. Sai dai gwamnatin Rasha ta musanta kai harin.