1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

MDD ta bukaci Isra'ila ta dakatar da cin zarafin Falasdinawa

Zainab Mohammed Abubakar
December 28, 2023

Galibin kashe-kashen da aka yi a Gabar Yamma da kogin Jordan na faruwa ne a lokacin da jami'an tsaron Isra'ila ke kai somame ko kuma arangama da mazauna yankin.

https://p.dw.com/p/4afEN
Hoto: MOHAMMED ABED/AFP

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya da aka wallafa a wannan Alhamis (28.12.2023) ya nuna rashin jin dadinsa kan abin da ya kira "tabarbarewar hakin bil adama" a yankunan gabar Yamma da Kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye, inda ya bukaci mahukuntan Isra'ila da su kawo karshen cin zarafin al'ummar Falasdinun da ke yankin.

Rahoton da ofishin hukumar kare hakkin bil adama ta OHCHR ya fitar ya ce an kashe Falasdinawa wajen 300 a yammacin gabar kogin Jordan tun a ranar da mayakan Hamas suka kai mummunan hari a kudancin Isra'ila daga Gaza da ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula kusan 1,200.