1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta bukaci sakin hambarerren shugaban Burkina Faso

February 11, 2022

Sama da makonni biyu da kifar da gwamnatin shugaban kasar Burkina Faso, kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya nuna damuwa da murkushe dimukuradiyya da sojoji suka yi.

https://p.dw.com/p/46rH2
USA New York | UN Sicherheitsrat -
Hoto: Richard Drew/AP/picture alliance

Yayin wani taron keke-da-keke, kasashe mambobin kwamitin na sulhu su 15 sun yi kiran sojojin na Burkina Faso da su gaggauta sakin  hambarerren Shugaba Roch Marc Christian Kabore da ke a hannunsu a yanzu.

Haka ma sun bukaci da a saki sauran jami'an tsohuwar gwamnatin na Burkina da suka kama a ranar 24 ga watan jiya.

Cikin watan Oktoba ne dai Sakatare Janar na Majalisar ta Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya bukaci mabobin na kwamitin sulhun, da su dauki matakin a kan yawan kwace iko da sojoji ke yi  wasu kasashen duniya.

 Kwamitin na sulhu wanda ke da cikakken ikon kakaba takunkumai ko daukar matakin soja a kan kasashe, na fama da rarrabuwar kawuna, musamman yadda Amirka da wasu kasashen ke jayayya da Rasha da kuma China.