Bukatar kaddamar da bincike a Burundi
July 14, 2020Talla
A cikin wata sanarwa da kwamitin bincike na MDD a kan Burundi ya bayyana ya bukaci sabon shugaban na Burundi Évariste Ndayishimiye ba da hadin kai wajen sake bude cibiyar kare hakin dan Adam ta majalisar a Burundi.Tun a shekara ta 2016 kwamitin kare hakin dan Adam na MDD ya soma gudanar da bincike a kan tafka ta'asa a Burundin. Tashin hankali biyo bayan zaben da aka yi a shekara ta 2015 mutane dubu 12 suka mutu, yayin da wasu dubu 400 suka yi kaura daga kasar.