Taro kan addinai da al'adun duniya
March 16, 2021Taron da ke zuwa a daidai lokacin da mabiya addinai musammama Musulmai a kasar China da Myanmar ke fuskantar tsangwama da kyama a yayin da kuma wasu masu tsaurin ra'ayin gaba da kowane irin addini ke kira ga gwamnatoti da su hana gudanar da addinai a doron kasa, bisa kasancewarsu dalilai na takurawa.
Majalisar Dinkin Dduniya ta bayyana cewa rashin sanin hakikakanin addini da mahimmancinsa wajen hade kan jama'a da tabbatar da zaman lafiya ne sa wasu mutane daukar irin wadannan matakan na wuce gona da iri.
Wadanda suka halarci taron sun hadu kan cimma wani kuduri na kasa da kasa da zai tilasta wa shuwagabannin kasashe kare addinai da al'adu, tare da sanyasu cikin abubuwa masu hurumi da ya zama wajibi a kiyaye kimarsu a duniya.
Kamar yadda ya nemi da a cusa a kidar jimirin girmama addini da al'adar da ta sabawa musamman ga matasa, da alhakin daukaka addini da al'ada da hanusu gurbacewa koma shafewa suka rataya kan wuyansu.
An nuna bukatar gabatar da shirye shirye da hudubobin addinai da za su sanya mabiya su rungumi akidar hakuri da zaman tare da mutunta juna, to amma kamar yadda sheikh Ateef Badwy na cibiyar binciken addini ta Al'azhar ke cewa wajibi ne a zamantar da irin wadannan shirye-shiryen tare da cewa "Matasan da ake fatan za su tasirantu da wadannan shirye-shiryen ba su da lokaci mai tsawo na zama suna sauraran wa'azi ko huduba, kamata yayi a yi amfani da shirye shirye masu kayatarwa da ke da gajeran zango ana yada masu su ta shafukan sada zumunta na zamani."