1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta tsawaita tukunkumai kan Sudan

March 9, 2023

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a yayin zaman sa na ranar Laraba 08.03.2023 ya tsawaita wa'adin takunkuman da aka saka wa kasar Sudan da shekara guda.

https://p.dw.com/p/4OQUx
Mata na karbar tallafin abinciHoto: Cai Yang/Xinhua/IMAGO

To sai dai kasashen Rasha da Chaina sun kaurace wa kuri'ar amincewa da matakin suna masu cewa ya kamata a cire wa kasar takunkuman da aka kakaba mata tun a shekarar 2005 sakamakon yakin Darfur.

Jerin takunkuman ciki har da na haramta wa Sudan sayen makamai ya raunana tattalin arzikin kasar da a halin yanzu ke zama mafi talauci a duniya, kuma juyin mulkin ranar 25 ga watan Oktoban shekarar 2021 ya kara dagula lamuran inda manyan kasashe suka janye tallafin da suke yi wa Khartoun din suna masu ikirarin sai kasar ta dawo kan tafarkin dumukuradiya.