MDD ta yaba yadda cutar Sida ke ja da baya a duniya
July 14, 2015Talla
Wata sanarwar hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da yaki da cutar ta fitar, ta ce an samu ragowa ta kashi 35 cikin 100 na yaduwar cutar a tsakanin shekaru 15. Ban Ki Moon ya yi wannan tsokaci ne daga birnin Addis Abeba inda ya ke halartar babban zaman taron mahawarar kasashen duniya kan samar da kudadan ayyukan cigaba.
Rahoto da Onusida hukumar MDD mai kula da yaki da cutar da Sida ta fitar a wannan Talatar a birnin Geneva wanda kuma Ban Ki Moon ya gabatar a gaban mahalarta taron na kasar Habasha, ya kara da cewa, idan ana so a cimma wannan buri na kawo karshen cutar nan zuwa shekara ta 2030, sai fa an kara kebe wasu kudade na milian dubu 32 na dollar Amirka a kowace shekara har ya zuwa shekara ta 2020.