Kashedi kan yiwuwar aukuwar fari a Somaliya
September 5, 2022Talla
Babban jami'in taimakon jinkai na Majalisar Dinkin Duniya Martin Griffiths ya shaida wa manema labarai cewa ya kadu matuka da abin da ya gani a 'yan kwanakin da suka wuce yayin ziyarar da ya kai Somaliya inda ya ga yara saboda galabaita ko kuka basa iya yi.
Akalla mutane kusan miliyan daya suka yi kaura daga muhallansu saboda fari a shekarun da suka wuce sakamakon tasirin sauyin yanayi da ya addabi yankin kahon Afirka da ya hada da Habasha da kuma Kenya.