MDD: Tallafin jin kai a Siriya
March 31, 2021Alkawarin bayar da tallafin zunzurutun kudin na zuwa ne bayan kammala taro tsakanin Majalisar dinkin duniya da kuma kungiyar Tarayyar Turai, inda Majalisar dinkin duniya ta yi fatan cimma matsayar hada dala biliyan goma.
Da tabbatar da alkawarin, Kwamishinan gudanar na EU Janez Lenarcic ya ce ba ya ga tallafin, cibiyoyin kudi da masu bayar da gudumawar sun bayar da rancen kudi har dala biliyan bakwai.
A cewar rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, fiye da rabin al'ummar kasar Siriya ne suke tsananin buktar tallafi yayin da aikin jin kai ke fuskantar tasgaro saboda annobar coronavirus. Kimanin mutane miliyan daya da rabi ne suka rasa rayukansu yayin da da dama ke gudun hijira a kasahen makwafta kawo yanzu tun bayan barkewar yakin basasa shekaru 10 da suka gabata a kasar.