1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yakin Ukraine ya mamaye taron MDD

September 21, 2022

Yakin Rasha da Ukraine da ya mamaye zauren taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 77, shugabanin duniya sun kuma nuna damuwarsu kan matsalolin sauyin yanayi.

https://p.dw.com/p/4H8Vg
USA I UN-Generalversammlung I Palästina
Hoto: Manuel Elias/UN Photo/Xinhua News Agency/picture alliance

A muhawarar da suka tafka a rana ta farko, shugabanin da za su kwashe tsawon mako guda suna tattaunawa sun nuna damuwa kan kalubalen da duniya ke fuskanta da suka hada da yunwa da matsalar sauyin yanayi da kuma irin illar da mamayar Rasha a Ukraine ta haifar na hauhauwar farashin kayayyaki da na abinci da ma makamashi.

Yayin da yake jawabi a zauren taron ta kafar bidiyo, shugaba Volodmyr Zelensky na Ukraine ya zargi Rasha da haifar da matsalar karancin cimaka da gangan. Ya kuma dora wa Moscow alhakin kawo cikas ga fitar da kayayyaki daga Ukraine da ke kan gaba wajen noma.

Shi ma da ya ke magana a kan batun cimaka, firanministan Spain Pedro Sanchez cewa ya yi, shugaba Vladmir Putin na yi wa kasashen duniya bita da kulli da batun abinci. Ya kuma kara da cewa babu zaman lafiya idan ana fama da yunwa, kazalika ba za a iya magance matsalar yunwa ba tare da zaman lafiya ba.

A nasa jawabin, firanministan Japan Fumio Kishida ya yi kira kan yi wa kwamittin sulhun Majalisar Dinkin Duniya garanbawul, ya bayyana rashin jin dadinsa kan gazawar da aka yi na mayar da martani ga mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine saboda kariyar da Rashar take da shi na kujerar dundundun a kwamitin sulhu.