1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta soki mahukuntan Iran

Zainab Mohammed Abubakar
November 24, 2022

Hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD ta yi Allah wadan afkawa masu zanga-zangar lumana biyo bayan mutuwar Mahsa Amini a Iran, inda ta kada kuri'ar amincewa yin bincike.

https://p.dw.com/p/4K1ce
UN Menschenrechtsrat | Volker Turk
Shugaban hukumar kare dan adam Volker TurkHoto: Martial Trezzini/KEYSTONE/picture alliance

Da kuri'un amincewa 25, da masu adawa shida a yayin da kasashe 16 suka kaurace wa zaben ne dai, hukumar kare hakkin dan Adam mafi girma ta MDD ta amince da kafa kwamitin kasa da kasa don binciken laifuffukan take hakkin bil'adama, da ake zargin Tehran da yi a matsayin martani kan masu zanga-zanga a kasar.

Tun da farko dai an yi fargabar cewar, Iran da kawayenta za su iya hana cimma wannan kudirin, sai dai tafi da shewa ya mamaye zauren taron bayan samun rinjayen masu amincewa da matakin.

An cimma kudirin ne a karshen zama na musamman da kasashen Jamus da Iceland da goyon bayan wasu kasashe 50 suka kira, don nazarin halin da Iran din ke ciki tsawon watanni biyu na zanga zanga bayan mutuwar Amini.