MDD za ta yi zama kan sabuwar fasahar AI
July 17, 2023Zaman da za a yi shi cikin wannan makon a birnin New York na kasar Amurka, Burtaniya ta yi kiran da a yi tattaunawa ta duniya baki daya, game da tasirin wannan sabuwar fasaha ta fuskan zaman lafiya da ma tsarin tsaro na duniyar.
Da ma dai gwamnatocin duniya na duba hanyoyin da za a bi, wajen rage hadarin fasahar ta Artificial Intelligence wanda ke da karfin sake fasalta tattalin arziki da tasro.
Burtaniya da ke rike da shugabancin kwamitin sulhun na Majalisar Dinkin Duniyar cikin wannan watan, na son a fito da tsarin yadda za a rika yi wa sabuwar fasahar linzami.
Cikin watan jiya ne Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya goyi bayan aniyar wasu shugabannin da suka samar da fasahar Artificial Intelligence wajen kawo na'urorin da za su rika sa ido kan ayyukan hukumomi irin su hukumar kula da makamashin nukiliyar duniya ta IAEA.