Me ya sa ba a sanya 'wrestlemania' a jerin wasannin Olympics
May 25, 2009Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun malam Murtala Ayuba daga ƙasar Ghana. Malamin cewa ya yi; Ku ba ni tarihin wasannin Olympics na duniya. Yau she aka fara shi? Kuma wace ƙasa ce ta fara karɓar baƙuncin sa. Kuma mene ne banbancin wasannin olympics na lokacin bazara da lokacin sanyi? Sannan kuma ku gaya min dalilin da ya sa ba a sanya wasan 'wrestling' irin su 'wrestlemania' a jerin wasannin olympics na duniya?
Amsa: Wasannin Olympics wasanni ne iri daban-daban na duniya da kwamitin wasannin Olympics na duniya yake shiryawa. Wasannin Olympics ya sami asali ne a tsohuwar Girika. Da can a tsohuwar Girka, a kan shirya wasanni a tsakanin dauloli daban- daban. Ana shirya waɗannan wasanni ne don bauta wa gumaka, shi ya sa wasannin ya ɗauki nau'i na addini, a sa'i ɗaya kuma, ana yin wasannin ne don inganta lafiyar jikin jama'a, saboda an sha samun yaƙe-yaƙe tsakanin daulolin.
Amma idan yaƙi ya barke a lokacin wasanni, to tilas ne ɓangarorin da yakin ya shafa su yi shelar dakatar da yaƙi. Saboda haka wasannin Olympics suna ɗaukar wata alama ta zaman lafiya. A kan yi wasannin da suka fi ƙasaita a wani wurin da ake kira Olympia wanda ke da nisan kilomita 360 daga birnin Athens, na ƙasar Girka, saboda haka aka sa wa wasannin suna Olympics.
An yi wasannin Olympics na karon farko a shekara ta 776 kafin haihuwar Yesu Almasihu ko Annabi Isa alaihissalam. To amma Bayan da tsohuwar daular Rum ta mamaye Girka, sai sarkin wancan lokaci ya soke dukan ayyuka na sauran addinai, kuma ya soke wasannin Olympics. Sai a shekarar 1888, Pierre De Coubertin, ɗan ƙasar Faransa ya ba da shawarar dawo da wasannin Olympics, kuma ba ma kawai 'yan ƙasar Girka ne ke iya shiga wasannin ba, mutane na ko wace ƙasa na iya shiga wasan duk da ƙabilunsu da launin fatarsu.
A shekara ta 1894, an tsai da kudurin kafa kwamitin wasannin Olympics na duniya a gun taron wasannin motsa jiki na duniya da aka yi Paris, daga baya an yi wasannin Olympics na karo na farko a zamanin yanzu daga ran 6 zuwa ran 15 ga watan Afril na shekara ta 1896. Wanda kasar Girka ta karɓi baƙuncin sa.
Wasannin Olympics na bazara da na sanyi
Tun daga shekarar 1896 har zuwa 1992 ana gudanar da wasannain Olympics ne duk bayan shekaru 4. To amma kasancewar wasannin Olympics sun rabu gida biyu, akwai na bazara da kuma na lokacin sanyi, wanda a baya duk ana yin su ne a cikin shekara guda, to daga shekarar 1994 sai aka dawo ana gudanar da wasannin duk bayan shekaru biyu. Na lokacin bazara daban, na lokacin sanyi ma daban.
Ya zuwa lokacin da aka rubuta wannan tarihi, wasan olympics na ƙarshe na bazara shi ne wanda aka gudanar a birnin Beijin na ƙasar China a shekara ta 2008. Wasan sanyi kuma za a gudanar da shi ne baɗi, a birnin Vancouver na ƙasar Kanada. Kuma banbancin su shi ne, su wasannin bazara na olympics wasanni ne na gamagari da za a iya yin su kowanne lokaci, su kuma wasannin sanyi, wasannin ne da ake yin su a cikin ƙanƙara.
Dangatakar Olympics da wrestlemania
To dangane da batun dalilin da ya sa ba a sanya wasan kokawa na Wrestlemania a jerin wasannin Olypcis shi ne, shi wrestlemania wasa ne da ake shirya shi domin nishaɗantarwa kawai, kuma ana shirya shi ne kamar yadda ake shirin film, wato ma'ana duk wasu doke-doke da ake yi a wreslemania an tsara su ne domin mutane su ga kamar gaske abin yana faruwa, amma a zahirin gaskiya shiri ne kawai.
Har ila yau kuma duk wani wasan kokawa na Wrestlemania, tun kafin a gudanar da shi, tuni an riga an shirya wanda zai ci nasara a wasan, kamar dai yadda a film ake tsara cewa, duk irin dukan da akai wa tauraron film wato actor, to ƙarshe sai ya girgije ya samu nasara akan basawa. wannan dalili ne ma ya sa aka canja sunan hukumar dake gudanar da shirn wasan wrestling daga sunan ta na asali WWF ( World Wrestling Federation) zuwa WWE (World Wrestling Entertainment). Wato ma'ana, wasan duniya na wrestling domin nishaɗantarwa.
Mawallafi: Abba Bashir
Edita: Umaru Aliyu