1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Medvedev a Gabas ta tsakiya

May 11, 2010

Rasha da Turkiya za su kulla dangantaka mai karfi, a lokacin Ziyarar Medvedev a Ankara

https://p.dw.com/p/NLal
Dmitry MedvedevHoto: AP

Shugaban ƙasar Rasha Dmitry Medvedev ya isa ƙasar Turkiya a wata ziyar da ake ganin za ta ƙarfafa hulɗa tsakanin ƙasashen biyu. Rohotanni suka ce a yayin wannan ziyarar, Mascow da Ankara za su sa hannu kan aikin ginawa Turkiya tashar makamashin nukiliya wanda Rasha za ta yi, kana kuma za su kulla yarjejeniyar da ta shafi kasuwanci tsakaninsu. Har ila yau ana saran za su sanya hannu kan yarjejeniyar baiwa 'yan ƙasashen biyu izinin tafiya ba tare da takardun visa ba a tsakainsu. Kafin ya Isa Ankara Medvedev ya kai ziyara a ƙasar Siriya wanda shine shugaban ƙasar Rasha na farko da ya kai ziyara a Siriya tun shekaru da dama. Kafin ya bar Damaskus, Medvedev ya kuma gana da shugaban ƙungiyar Hamas Khalid Mashal wanda yake zama a Siriya, inda shugaban kasar ta Rasha ya nemi Hamas da ta sako sojan Isra'ila dake hannunta.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu