1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel a yammacin Afirka ta dau hankalin jaridun Jamus

Usman Shehu Usman YB
May 3, 2019

Kasashe uku da Angela Merkel ta kai ziyara, Burkina Faso da Nijar da Mali a bisa kiyasin MDD kasashen uku na a cikin kasashe mafiya talauci.

https://p.dw.com/p/3HuJW
Afrika Burkina Faso l Kanzlerin Angela Merkel trifft Präsident Roch Marc Kabore
Hoto: picture alliance/dpa/M. Kappeler

A Jaridun wannan mako za mu fara ne da Frankfurter Allgemeine Zeitung wace ta yi labari kan ziyarar Angela Merkel a wasu kasashen Yammacin Afirka. Jaridar ta ce Merkel ta kai ziyara a yankin Sahel wanda a yanzu ya kasance kan gaba cikin harkokakin kasashen waje na Jamus. Kasashe uku da Merkel ta kai ziyara, Burkina Faso da Nijar da Mali, ana iya saka su a saman farko. A bisa kiyasin MDD kasashen uku suna cikin sahun karshen na kasashe mafiya talauci a duniya. Duk kuwa da kokarin da kasashen Jamus da Tarayyar Turai ke yi na samar da zaman lafiya a yankin, batun tsaro sai kara tabarbarewa yake yi a kasashen. Misali a Burkina Faso ko da wannan Litinin 'yan ta'adda sun kai hari wa coci guda uku inda suka kashe fasto daya da wasu mabiya hudu.

Niger Kanzlerin Merkel auf Afrikareise | Merkel und Präsident Issoufou
Angela Merkel da Mahamadou Issoufou a birnin YamaiHoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung ta duba kasar Sudan ne, inda ta ce a Sudan yanzu lokaci ne a hade ko a watse. Walau dai ko masu bore su tilasta wa sojoji mika mulki, ko kuma sojojin su sake dare mulki kamar yadda ta faru kusan shekaru 30 da suka gabata. Sojojin da ke mulki sun bayyanan cewa sun cimma matsaya tsakaninsu da masu boren za'a kawo karshen boren inda za a bude gadoji da titunan da aka rufe tun fara boren da ya yi sanadiyar kifar da gwamnatin Umar al-Bashir. Sai dai za a ci gaba da yin zaman dirshan a harabar hedikwatar sojojin.

Za mu karkare da jaridar Neue Zürcher Zeitung wacce ta yi labarinta bisa Caster Semenya, 'yar wasannin guje-guje. Bayan kimanin shekaru 10 ana tafka shari'a kotu da ta yi watsi da daukaka karar da Semenya ta yi kan dokar rage kwayoyin halittar maza a jikin mata masu wasannin guje-guje. Wannan shari'a dai yanzu ta bar baya da kura sakamakon yadda Caster Semenya 'yar kasar Afirka ta Kudu kuma wacce ta yi nasara har sau biyu a tsaren gudun wasannin Olympics ba ta yi nasara a shari'ar da ta daukaka ba.