Bincike ya nuna Merkel ba ta da coronavirus
March 23, 2020Talla
Tun daga farko kakakinta ya ce shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na nan lafiya kalau kana kuma tana ci gaba da aikinta a gida bayan ta killace kanta, sannan ya ce za a ci gaba da sauran gwaje-gwaje nan da gaba kan shugabar gwamnati, bayan binciken farko ya nuna cewa bata dauke da kwayoyin cutar.
Da sanyin safuyar yau Litinin shugabar gwamnatin ta halarci wani taron majalisar minitocin kasar ta wayar tarho inda gwamnatin ta dauki wasu muhimman matakai game da batun tattalin arziki.
Kawo yanzu fiye da mutun dubu 22 da 670 ne suka harbu da cutar a Jamus wasu 86 suka rigamu gidan gaskiya a cewar wata cibiar bincike ta Robert Koch Institut.