1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta ce da Turkiyya Ahir kan kalaman Nazi

March 20, 2017

Yayin da dangantakar Jamus da Turkiyya ke kara yin tsami mahukuntan kasar ta Jamus sun ja kunnen Turkiyya ta kiyayi danganta shugabar gwamnati da kamalaman Nazi

https://p.dw.com/p/2ZZ5N
Merkel und Erdogan
Hoto: picture-alliance/dpa

Jamus ta ce ko kadan ba za ta lamunci kalaman batanci daga shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ba na kwatanta shugabar gwamnati Angela Merkel da daukar matakai irin na Nazi.

Turkiyya dai na takun saka da wasu kasashenTurai musamman Jamus wadda ke da turkawa masu yawa a cikinta gabanin zaben raba gardama da za'a kada a ranar 16 ga watan Aprilu na neman yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulki domin baiwa Erdogan karin karfin iko.

Erdogan ya yi wadannan kalamai ne akan Merkel a karshen mako bayan da hukumomin Jamus suka ki amincewa ministocin Turkiya su gudanar da yakin neman zabe a cikin kasar.

Mai magana da yawun Merkel Ulrike Demmer ta fada a ranar litinin din nan cewa gwamnati na bi sau da kafa irin kalaman Erdogan kuma ba za'a lamunci dukkan wani kwatance da akidar Nazi ba.