Merkel ba ta yi nadama a kulla cinikayar gas da Rasha ba
October 13, 2022Angela Merkel ta kare matsayarta da cewar kulla yarjejeniyar sayen gas a wancan lokacin da kasar Rasha ya fi sauki da kuma saurin samu idan aka kwatanta da dauko shi daga wasu kasashen duniya kamar Amirka da Saudiyya ko kuma daga kasar Qatar.
Dogaro da Rasha a matsayin kasa daya tilo da ke samar da mafi yawan makamashin da Jamus ke amfani da shi ya jefa kasar cikin mawuyacin hali.
Yanzu haka dai Jamus kasa mai karfin tattalin arziki a nahiyar Turai na fadi tashin ganin ta samar da isasshen makamashin ga al'ummarta, wanda tun bayan da dangantaka ta yi tsami a tsakanin kasashen yamma da Rasha makamashin ya yi karanci a nahiyar.
Sai dai ko a rana Laraba Shugaba Vladmir Putin na Rasha ya yi tayin bude bututun Nord Stream da ke dakon makamashi daga kasarsa zuwa Turai ta kasar Jamus, amma mahukuntan na Jamus sun yi watsi da tayin nasa.