1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Angela Merrkel ta zanta rikicin Isra'ila da Falastinawa

Abdoulaye Mamane Amadou
May 20, 2021

A yayin da rikicin Isra'ila da kungiyar Hamas mai iko da Zirin Gaza ke ci gaba da kisan rayukan jama'a, shugabar gwamnatin Jamus da Mahmud Abbas sun duba hanyoyin tsagaita wuta.

https://p.dw.com/p/3tgtt
Berlin Abbas bei Merkel
Hoto: Reuters/P. Kopczynski

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta tattauna ta wayar tarho da Firaministan Falasdinu Mahmud Abbas a wannan Alhamis ta wayar tarho, da zummar duba yiwuwar cimma duk wasu hanyoyi na tsagaita wuta a batakashin da ake yi tsakanin Palasdinawa da Isra'ila.

Tun daga farko dai Merkel, ta bayyana cewa a share daya tana goyon bayan matakin Isra'ila na kare kanta, biyo bayan cinna rokokin da ta ce mayakan Hams na yi mata daga Gaza, a cewar wata sanarwa da kakakinta Steffen Seibert ya bayyanawa manema labarai.

Ko a wannan Alhamis Falasdinawa biyar aka tabbatar da sun hallaka, biyo bayan wani harin Isra'ila a yankin na Zirin Gaza.