Ganawar Merkel da Hollande da Renzi
June 27, 2016Kwanaki hudu bayan da 'yan Birtaniya suka zabi ficewa daga Kungiyar Tarayyara Turai wato EU, a yanzu haka kasashen Turai na ci gaba da nazarin hanyoyin diplomasiyya na gaggauta daukar matakan aiwatar da matakin raba gari da Birtaniyar da kuma na ceto kungiyar ta EU. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel za ta karbi bakuncin shugaban kasar Faransa Francois Hollande da kuma Firaministan Italiya Matteo Renzi a Birnin Berlin fadar gwamnatin kasar, da nufin yin nazari dangane da ficewar Birtaniya daga kungiyar Tarayyar Turai gabanin taron koli na kungiyar ta EU da za su gudanar a ranar Talata 28 ga wannan wata na Yuni da muke ciki, inda kasashen Kungiyar za su tattauna kan matakan da suka dace su dauka domin sake farfado da matsayin kungiyar bayan ficewar Birtaniyan.