Merkel da Putin sun gana kan rikicin Ukraine
July 13, 2014Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da kuma Shugaba Vladimir Putin na Rasha sun amince kan cewa rikicin Ukraine na da matukar illah kuma sun bukaci da a mayar da hankali sosai kan batun sulhu. Kakakin shugaban kasar Rasha Dmitry Peskov ne ya sanar da hakan inda ya ce shugabannin biyu sun cimma wannan matsayar ne yayin 'yar takaitacciyar ganawar da suka yi a Brazil gabanin wasan karshe da za a fafata tsakanin Jamus din da Argentina. Da ma dai shugabannin biyu sun saba tattaunawa kan batun na Ukraine ta wayar tarho inda Merkel ta bukaci Putin da ya yi amfani da damar fada a jin da yake da ita a gabashin Ukraine domin kawo karshen rikicin da ake fama da shi a yankin tsakanin dakarun gwamnatin Kiev da 'yan aware masu goyon bayan Rasha.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal