Jamus da Rasha za su karfafa dangantaka.
August 18, 2018Talla
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce rikicin da yanzu haka ke wakana a Siriya da dambarwar da ake a gabashin Ukraine da kuma takun sakar Amirka da Iran na kan sahun gaba kan batutuwa da ita da takwaranta na Rasha Shugaban Putin na Rasha za su maida hankali a kai.
Baya ga wadannan batutuwa, Merkel ta ce ta tabo batun kare hakkin dan Adam a kasar Rasha da kuma ma kuma dangantaka da ke akwai tsakanin kasashen biyu wanda ke da karfin fada a ji a duniya.
Shugabar ta gwamnatin Jamus ta ce a ganinta abubuwa masu sarkakiya na bukatar a hau kan teburin tattaunawa a kuma yi amfani da masalaha wajen warwaresu. Wannan ne ma ya sanya ta ce ta ga dacewar tattaunawa kan wadanan batutuwan da shugaban na Rasha a ziyarar ya kawo a Jamus.