1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel da Sarkozy za su tallafa wa Girka

June 17, 2011

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da kuma shugaban Faransa Nicolas sarkozy sun gudanar da taron manima labarai a Berlin, inda suka yi alƙawarin samar da hanyayoyin taimaka wa Girka tayar da arzikinta cikin gaggawa.

https://p.dw.com/p/11dj8
Angela Merkel ta Jamus da Nicolas Sarkozy na Faransa a birnin BerlinHoto: picture alliance/dpa

Shugaba Nicolas Sarkozy na ƙasar Faransa ya ganawa da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a birnin Berlin, a inda suka tattaunawa game da yadda za a ceto ƙasar Girka daga halin koma bayan tattalin arziki da ta samu kanta a ciki. Wannan ziyarar ta sarkozy ta zo ne a daidai lokacin da fadar mulki ta Paris ta nunar da fargaba dangane da asarar da ƙasashen da ke amfani da Euro za su tafka idan suka bai wa Girka bashin kuɗin da nufin tallafa mata. Sai dai shugaabannin biyu sun amince da samar da hanyoyin gaggawa domin taimaka wa ƙasar Girka da ta shawo matsalar basusukan da take fama da su, wanda suka janyowa ƙasar karayar tattalin Arziki.

Sakataren ma' aikatar harkokin wajen Jamus Werner Hoya ya bayyana fatan cewa kasashen 2 zasu cimma matsaya game da matakan da ya kamata a ɗauka domin tayar da komaɗar tattaliin arzikin Girka. Werner ya shaidawa gidan talabijin ɗin jamus cewar ƙasashen biyu suna da matukar sha'awar tayar da darajar kuɗin Euro da ke cikin mawuyacin hali. Merkel da Sarkazy har ila yau sun tattauna akan rikicin shugabancin asusun ba da lamuni na duniya wato IMF, inda ƙasashen biyu ke goyon bayan ministar kuɗin Faransa Christine Lagarde.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Umaru Aliyu