1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Angela Merkel ta ce Jamus bata taba fuskantar wani yanayi

Abdoulaye Mamane Amadou
March 19, 2020

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce Jamus bata taba fuskantar wani mawuyacin kalubale kamar irin wanda take ciki ba a yanzu tun bayan yakin duniya na biyu saboda annobar Coronavirus.

https://p.dw.com/p/3ZgZ5
Deutschland Berlin | Coronavirus | Ansprache Angela Merkel, Bundeskanzlerin
Hoto: picture-alliance/dpa/Bundesregierung/S. Kugler

A cikin jawabinta ga 'yan kasar ta gidajen talabijin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta shawarce 'yan kasar su da su yi kokari su bi shawarwari da hukumomin suka sanya don yaki da cutar coronavisrus da ke dada kamari a kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Jamus DPA ya ce idan har Jamusawa suka bijirewa matakan kariya da mahukumta suka dgindaya to akwai yiwuwar cutar ta harbi mutum akalla milyan10 nan da wasu watanni masu zuwa kamar yadda wani bincike da wata cibiyar kasar ta gudanar.

Kawo yanzu dai mutane sama da dubu sha biyu da dari uku da ashirin da bakwai ne (12,327) ke dauke da cutar a Jamus.