1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel na shirin tarbar Tsipras

Pinado Abdou WabaMarch 23, 2015

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na so ta ji irin sauyin da gwamnatin Alexis Tsipras za ta yi dangane da tattalin arziki

https://p.dw.com/p/1Evlo
Belgien Merkel und Tsipras beim EU-Gipfel
Hoto: picture-alliance/AA

Da yaman nan ne Firaministan Girka Alexis Tsipras ke kai ziyararsa ta farko a Berlin. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi mi shi karbuwa na musamman da wani fareti na karramawa. Kan gaba a kan batutuwan da za su tattauna shi ne siyasar sauye-sauyen da ake bukatar ganin Girkar ta aiwatar, wanda kuma yake cigaba da janyo cece-kuce tsakanin kasashen Turan musamman Jamus. Bayan cacar bakar da bangarorin suka yi daga karshen makon da ya gabata, yanzu sun shirya su cimma matsaya.

A karshen wata tattaunawa da ya yi da takwaransa na Girka Nikos Kotzias a Berlin, ministan kula da harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeier ya shawarci duk bangarorin su yi kokari su rika fahimtar juna ko a wannan lokacin da suke da babbar matsalar da ke bukatar sulhu cikin kankanin lokaci