Merkel na son tsaurara yaki da corona
December 9, 2020Talla
A yayin ta gabata a gaban majalisar dokokin Jamus, Angela Merkel ta bukaci da a duba yiwuwar karfafa matakan dakile yaduwar annobar corona a Jamus, ciki har da da kara rage adadin wadanda ka iya haduwa wuri guda a gabanin bukukuwan Kiristmetin da ke tafe, da ma duba yuwuwar shiga hutun 'yan makaranta da wuri.
Haka shi ma ministan harkokin lafiyar Jamus ya bayyana muhimmancin daukar matakan yaki da annobar musamman ma a yankunan da aka samu mutun 200 daga cikin dubu 100 da suka kamu da annobar.