Merkel na wata ziyarar aiki a yankin Kaukasiya
August 23, 2018Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a wannan Alhamis ta gana da shugaban kasar Jojiya Giorgi Margvelashvili a birnin Tiblisi da ke zama zangon farko na rangadin da take kaiwa yankin kudanci Kaukasiya.
Shugaba Margvelashvili ya yi amfani da wannan dama ya jadadda muhimmancin goyon bayan da Jamus ke ba wa Jojiya inda ya ce.
"Shugabar gwamnati da tawagarki ina mai mika farin cikinmu ga wannan muhimmiyar ziyara da muka samu daga kawayenmu Jamusawa. Jamus ta kasance babbar mai tallafa wa Jojiya tsawon shekaru, wato tun daga farkon samun 'yancin kanmu, Jamus ta zama ja-gaba wajen taimaka wa ci-gaban kasarmu."
A nata bangaren Merkel ta goyi bayan a ba wa Jojiya matsayin kasa mai kwanciyar hankali da lumana ga masu neman mafakar siyasa. Ta ce yawan 'yan kasar da ke neman mafakar siyasa ya ragu.
Jojiya da ke zama tsohuwar daula a tsohuwar Tarayyar Sobiet tana da burin samun wakilci a kungiyoyin EU da NATO. Merkel za ta kai kuma ziyara a kasashen Armeniya da Azerbaijan.