Merkel ta kai ziyara Saudiyya
April 30, 2017Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta sauka birnin Jiddah domin tattaunawa da mahukuntan Daular Saudiyyar kan batutuwa da suka kama daga yaki da kungiyar IS da kuma dumamar duniya.
Ziyarar ta yini daya na zuwa ne yayin da Merkel ke kara kaimi na matakan diflomasiyya gabanin taron kungiyar G20 ta kasashe masu cigaban masana'antu na duniya wanda Jamus za ta karbi bakuncinsa a bana.
A ranar litinin kuma shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel za ta wuce kasar hadaddiyar daular larabawa inda za ta gana da yarima Sheikh Mohammed bin Zayed Al-Nahyan sannan ta gana da shugaban Rasha Vladimir Putin a birnin Sochi a ranar Talata.
Merkel za ta bukaci yin matsin lamba ga saudiyya ta sassauta matakinta kan shingen cinikayya. Yayin da a waje guda kuma ake sa ran za ta tabo batun kare hakkin dan Adam da gudunmawar mata tare da Sarki Salman da kuma yarima Mohammed bin Nahyan