Shugaba Merkel ta kadu da ta'asar ambaliya
July 18, 2021Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta fara ziyarar yankunan kasar da iftila'in ambaliyar ruwa ya afkawa a wannan Lahadin. Merkel da ke wata ziyarar aiki a Amirka a lokacin iftala'in, ta kai ziyarar gani da ido a Schuld da ke yankin Ahrweiler, inda mutum 110 suka mutu a sakamakon ambaliyar a kauyen da al'umarsa ba su zarta 700 ba. Merkel ta baiyana kaduwa bayan gane ma idanunta ta'asar ambaliyar.
Tare da rakiyar gwamnan jihar Rhineland-Palatinate, Malu Dreyer da magajin garin na Schuld, Helmut Lussi sun tattauna da masu aikin ceto da kuma sauran jama'ar da matsalar ta shafa. A garin Erftstadt da ya fuskanci matsalar ambaliya mafi muni a tarihinsa, mutum kimanin 60 ne suka bata, a can jahar Bavariya da ke iyaka da kasar Ostiriya, an kwashe sama da mutane 100 daga gidajensu, a sakamakon ta'addin mamakon ruwan saman. Jimillar mutane 183 kawo yanzu, aka tabbatar da mutuwarsu sakamkon ambaliyar. Shugabar gwamnatin ta ce za a gaggauta wadata jama'a da duk irin tallafin da suke bukata kamar yada ta fadi a farkon makon nan.