Merkel ta alkawarta ba da taimako ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Jamus
June 5, 2013Talla
Merkel ta ce tuni gwamnatin Tarayyar ta Jamus ta kebe Euro miliyan dari domin ba da wannan taimakon gaggawa daidai wa daida ga yankunan Bavariya da Saxony da kuma Thueringen da bala'in ambaliyar ruwan ya shafa. Merkel ta kuma ba da tabbacin duba yiwuwar ba da karin taimako in har wadannan kudade suka kasa. Ko da yake sannu a hankali ana samun raguwar ambaliyar a kudancin kasar to amma har yanzu da wasu wurare da ke cikin mawuyacin hali. Shugaban kasar Jamus, Joachim Gauck ya mika godiyarsa ga 'yan kwana-kwana bisa aikin da suka yi babu gajiyawa domin taimaka ma wadanda bala'in ya shafa.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal