Merkel ta yi kira ga kawo sauyi a kungiyoyin duniya
January 23, 2019A jawabin da ta gabatar a wannan Laraba a taron tattalin arzikin duniya da ke ci gaba da gudana yanzu haka a birnin Davos na kasar Switzerland, Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana damuwarta dangane da jan kafan da manyan kungiyoyin duniya ke yi wajen aiwatar da sauye-sauyen da ake jira daga garesu:
Ta ce "Mun lura da cewa dukkanin kungiyoyi na duniya na fuskantar matsala wajen aiwatar da sauyi, inda ala misali muka kwashe shekaru masu yawa kafin mu kai ga aiwatar da shirin sauya fasalin Asusun Ba da Lamuni na Duniya, ga shi a yanzu ma akwai matsala ga batun kara jarin Bankin Duniya"
Merkel ta kuma yi gargadin kan bukatar aiwatar da wadannan sauye-sauye cikin gaggawa domin a cewarta tattalin arzikin kasashe masu tasowa irinsu Chaina da Indiya na yin tasiri ga tattalin arzikin duniya baki daya.
Kuma a cewarta matsawar manyan kasashen duniya musamman na Turai ba su gaggauta aiwatar da sauye-sauye a kungiyoyinsu ba, to kuwa dole a samu bayyana wasu sabbin kungiyoyin na duniya kamar yadda aka samu bayyana Bankin kasuwancin kasashen nahiyar Asiya dabra da Bankin Duniyan, ko kuma kokarin da Chaina ke yi na kafa sabon kawancen kasuwanci na musamman da wasu kasashen Turai 16. Kazalika Merkel ta ce manyan kalubalai kamar na gurbatar muhalli ko kuma kutsen Intanet matsaloli ne da ke bukatar hadin kai idan ana son shawo kansu.