Merkel ta bukaci yin gyara ga yarjejeniyar EU
November 7, 2012Wannan shiri zai hada ne da yin sauye-sauye a yarjejeniyar kungiyar domin kau da kurakuran da aka tafka a fannin tattalin arziki da kuma yin amfani da kudi na bai daya. A cikin jawabinta da ke zaman irinsa na farko da ta yi a gaban 'yan majalisar dokokin Turai cikin shekaru biyar ta ce tana ba da muhimmaci ga bukatar yin takara a manufar tattalin arziki na kasashen Kungiyar Tarayyar Turai(EU). A taron da zai gudana a watan Disamba ne dai Merkel za ta tsai da shawarar yin gyaran fuska ga manufar yin amfani da takadar kudi ta bai daya.
A cikin jawabin da ta yi a birnin Brussels na kasar Beljiyam, Merkel ta ce akwai bukatar daukar kwararan matakai da za a zartar cikin shekaru biyu ko uku masu zuwa. Ta kuma bukaci samar da karin 'yanci sa ido akan duk wani aiki hadin-gwiwa da za a yi a kungiyance ko kuma a matsayin daidaikun kasashe.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Dan-Ladi Aliyu