Merkel ta kai ziyara yankin Balkan kan shigarsu EU
July 9, 2015Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce za ta taimaka wa Bosniya da ke sahun karshe a jerin kasashen yankin Balkan da ke son shiga kungiyar Tarayyar Turai, ta gaggauta shirye-shiryen samun wakilci a kungiyar ta EU. Merkel wadda ke halartar bikin cika shekaru 20 da kisan kiyashin Srebrenica lokacin da sojojin Sabiyawan Bosniya suka kashe Musulmi dubu takwas ta ce akwai matsaloli a Bosniya da ya kamata a warware tukuna.
"Muna goyon bayan muradun dukkan kasashen yankin Balkan game da Turai, mun kuma san da matsaloli da yawa da ya kamata a warware su a Bosniya. Yankin gaba daya zai bunkasa ne idan Bosniya ta samu kyakkyawan cigaba."
A bara Jamus da Birtaniyya sun kaddamar da wani shirin farfado da burin Bosniya na shiga kungiyar EU, inda suka mayar da hankali kan sauye-sauyen tattalin arziki da zamantakewa maimakon batutuwan da suka raba kan 'yan siyasar kasar.