1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta jaddada bukatar kasuwancin bai daya

Abdul-raheem Hassan
January 24, 2018

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta caccaki manufofin shugaban Amirka Donald Trump da ke adawa da tsarin kasuwancin bai daya.

https://p.dw.com/p/2rTAS
Weltwirtschaftsforum 2018 in Davos | Angela Merkel
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Schreiber

A ci gaba da taron tattalin arzikin duniya da ke gudana a birnin Davos na kasar Switzerland, shugabannin duniya na kara jaddada muhimmancin cudanya da juna don karfafa tattalin arziki.

Merkel ta bayyana a taron cewa kebewa da kariya, ba shi ne mafita kan kalubale da ke fuskantar tattalin arzikin kasashen duniya a halin yanzu ba.

"Mun yi imnin cewa tsarin wariya ba zai kaimu ko ina ba, amma batu ne na samar da gurbin kasuwanci da zai habaka tattalin arziki kamar yadda muke fata. Jamus na fatan cimma wannan tsari, idan an yadda cewar kafa gwamnati a Jamus zai taimaka, to tabbas za a samu ci gaba fiye da haka."

Merkel ta bayyana kudirinta na ganin kungiyar Tarayyar Turai ta cimma kulla yarjejeniyar kasuwanci da Birtaniya idan ta fice daga EU, sai dai ta ce kungiyar EU ba za ta sauya matsayar ta a kan wasu tsare-tsaren ballewar Birtaniyar ba.