1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta kai ziyara Aljeriya

September 17, 2018

Shugabar gwamnatin Jamus Angeka Merkel, ta kai ziyara kasar Aljeriya inda za ta duba matsalolin baki haure da kuma na tsaro.

https://p.dw.com/p/350bt
Algerien Besuch Bundeskanzlerin Merkel
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

Shugabar gwamnatin Jamus Angeka Merkel, ta kai ziyara kasar Aljeriya a yau Litinin, inda za ta tattauna da Shugaba Abdelaziz Bouteflika kan hanyoyin dakile matsalolin nan na bakin haure da kuma na tsaro.

Haka nan ana sa ran shugabannin biyu za su tabo batun rawar da Aljeriya ke takawa tsakanin kasashen arewacin Afirka.

Angela Merkel za kuma ta gana da Firaminista Ahmed Ouyahia lokacin ziyarar ta yini guda, sai kuma rikicin nan da ke tsakanin kasar ta Aljeriya da kuma makwabciyarta Moroko.

Dama dai a cikin watan Fabrairun bana ne shugabar gwamnatin ta Jamus za ta kai wannan ziyara, amma aka soke ta saboda rashin lafiyar shugaban na Aljeriya, Abdelaziz Bouteflika mai shekaru 81, wanda ke mulki tun cikin shekarar 1999.