1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta kammala ziyara a gonar Bush

November 11, 2007
https://p.dw.com/p/CABj

SGJ Angela Merkel da shugaban Amirka GWB sun ce dukkansu sun kuduri aniyar yin aiki tare don warware takaddamar da ake yi da Iran dangane da shirin ta nukiliya ta hanyar diplomasiya. A karshen ziyarar da ta kai a gonar shugaba Bush dake jihar Texas, Merkel ta fadawa manema labarai cewa Jamus ka iya goyon bayan karin takunkumai da za´a sanyawa Iran idan gwamnati a birnin Teheran ta ci-gaba da yiwa gamaiyar kasa da kasa kunnen uwar shegu.

Merkel:

Ta ce “Shirin nukiliyar Iran wata babbar barazana ce, to amma dukkan mu mun yi imanin cewa za´a iya shawo kan wannan barazana ta hanyar diplomasiya. A dangane da haka mun yanke shawarar daukar matakai na gaba.”

Yayin ziyarar ta tsawon sa´o´i 20 Merkel ta kuma jaddada bukatar Jamus na samun kujerar dindindin a kwamitin sulhun MDD, to amma shugaban na Amirka bai ce ko zai goyi da bayan wannan mataki ba.